Labarai
Rundunar yan sanda ta hana jami’an KAROTA da na Vigilante zuwa wajen zaɓe

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta haramta wa jami’an KAROTA da ’yan sa-kai na kungiyar Vigilante, shiga wuraren zaɓe a yayin zaɓen cike gurbi da za a gudanar a kananan hukumomin Ghari, Tsanyawa, Bagwai da Shanono a gobe Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar a daren jiya Alhamis a madadin kwamishinan ’yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori.
Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne tare da sauran matakan tsaro domin gudanar da zaɓen cikin lumana, adalci da gaskiya.
Ta kuma bayyana cewa zirga-zirgar motocin hawa, Adaidaita Sahu da babura za a takaita su daga ƙarfe 12:00 na tsakar daren Juma’a zuwa ƙarfe 6:00 na yamman ranar zaɓen, sai dai ban da motocin ayyukan gaggawa, motocin hukumar zaɓe da masu sa ido da aka amince da su.
You must be logged in to post a comment Login