Kiwon Lafiya
Rundunar yan sanda ta kame a kalla mutans 145 bisa zargin tashe-tashen hankulan jihar Benue
Akalla mutane 145 Rundunar ‘yan-sanda ta cafke bisa zarginsu da hannu cikin tashin hankalin da ke faruwa a Jihar Benue, inda aka gurfanar da 124 daga cikinsu gaban kuliya.
Goma sha shida daga cikinsu an zarge su da hannu cikin rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu Fulani 7 a garin Gboko na Jihar ta Benue a ranar 31 ga watan jiya.
Wadannan bayanai na kunshe cikin kunshin bayan da babban Sufeton ‘yan-sandan kasar Ibrahim Idris ya gabatarwa kwamitin hadin gwiwa kan harkokin tsaro na Majalisar Dattijai a ranar Juma’ar da ta gabata.
Gwamnan Jihar ta Benue Samuel Ortom y adage dokar hana zirga-zirgar da ya sanya a garin Gboko, kamar yadda mashawarcin gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai Tahav Agerzua ya sanar.