Labaran Kano
Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta ja hankali alumma kan zaben ranar Asabar
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishinanta Cp Habu A. Sani, na sanar da al’ummar Jihar Kano cewa, hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC zata sake gudanar da zabuka Ranar Asabar 25/01/2020 a Kananan hukumomin Bebeji, Tudun Wada, Doguwa, Rogo, Kumbotso, Kiru, Bunkure, Minjibir da kuma Karamar Hukumar Madobi.
Hukumar na bada tabbacin cewa tayi hadin kai da takwarorin hukumomin tsaro dake nan Kano domin tabbatar da anyi zabe lafiya an kuma gama lafiya,
A don haka, al’umma su tabbata sun kiyaye da wasu daga cikin sharudan da ta gidanya don samun nasarar zaben da suka hadar da,duk wani motsin ababen hawa kamar Motoci, Adaidaita Sahu da Babura an haramta shi tun daga daren jajiberen ranar zaben har a kammala a wadannan kananan Hukumomi Guda Tara da za’ayi zabe, in banda motocin Asibiti, Jami’an Kashe Gobara, Ma’aikatan zabe da wadanda hukumar zaben ta tantance.
Haka zalika rundunar bata yarda duk wasu matasa yan tada zaune tsaye su kusanci inda ake gudanar da zaben ba.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da kakkin rundunar ‘yan sand ana jihar DSP Abdullahi Haruna ya sanyawa hannu cewa, ta hana daukar duk wani makami ko kuma abun cutarwa a yayin gudanar da zaben, jami’an tsaro ba za su amince da haka ba.
Haka kuma Iya wadanda suka cancanci zabe za’a bari a harabar zaben.
Bugu da kari da duk wanda bashi da katin zabe da yake nuna lambar akwatin zabensa a wannan yanki, hukuma zatayi awon gaba dashi.
Dangane da haka rundunar bata aminta da kawo wani mutum ko wasu mutane inda ake zaben ba. Matukar ba hukumar INEC ce ta tantance suba sannan iya wakilan Jam’iyyun da hukumar zabe ta tantance aka amince da zuwan su zaben.
Daga karshe rundunar ‘Yan sanda ta Jihar Kano na yiwa al’umma fatan yin zabe lafiya kuma a gama lafiya.
A Don neman taimakon gaggawa ko kuma sanar da faruwar wani lamari, sai a kira wadannan lambobin 08032419754, 09029292926, 08123821575.