Labarai
Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane
Rundunar ‘yansandan ta jihar Kano tayi holin wasu mutane da take zargi da laifukan yin garkuwa da mutane da yin fashi da makami, da kuma satar ababan hawa da kuma safarar miyagun kwayoyi a jihar Kano.
Sabon Komishinan ‘yansandan na jihar Kano CP Habu Ahmad Sani, ya sanar da hakan yayin da yake holen kayayyakin laifukan da kuma mutane da ake zargi a yau Laraba a shelkwatar rundunar ‘yan sanda dake nan
Kazlika kwamishinan ‘yan sandan Habu Ahamad Sani, ya ce rundunar zata cigaba da kama masu laifi a duk inda suke don ganin zaman lafiya ya wanzu a jihar Kano da ma kasa baki daya.
Kano: Lauyoyi sun yi barazanar gurfanar da kwamishinan ‘yan sanda
Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda
Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra
Wasu daga cikin wadanda ake zargin sun yin a dama yayin da kuma wasu daga ciki ke bayyana irin dalilan da ya sanya jami’an ‘yan sandan suka kama su.
Har ila yau wasu daga cikin wadanda ake zargin sun ce sun taka sahun barawo ne amma kuma sun na damar aikata hakan.
A hannu guda kuma wasu ana zargin su ne da siyan kayayyakin sata.
Wakilin mu Abba Isah ya ruwaito cewa komishinan ‘yansandan Kano Habu Ahmad Sani, ya yi kira ga alummar jihar Kano da dinga tallafawa jami’an tsaro ganin lamarin tsaro na bukatar masu ruwa da tsaki kuma na kowa da kowa ne, a don haka na bukatar gudunmawar kowa da kowa.