Labarai
Rundunar yan sanda ta sallami jami’anta uku bisa laifin barnatar da harsashi ba bisa ka’ida ba
Rundunar yan sandan jihar Lagos ta kori wasu yansanda uku, biyu masu mukamin Sergent da kuma kofur guda daya bisa laifin barnatar da harsashi ba bisa ka’ida ba.
Yan sandan sun hadar da Sajan Saturday Osaseri da kuma sajan Segun Okun sai kuma kofur Adekunle Oluwarotimi bayan gurfanar da su gaban kwamitin da’a na rundunar yan sandan inda kwamitin ya ce yan sandan sun karya tsarin rundunar yan sandan.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan da ke Lagos SP Chike Oti ya ce wadanda ake zargi da aikata laifin sun aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Janairu da misalin karfe 9 da rabi na dare a kan titin Amukoko.
Oti ya ce yadda yan sandan sukayi harbi da bindigogin su akan wasu matasa da ke zargin sun jefe su da duwatsu da rabar ruwa ya saba ka’ida.
Ya ce hakan ya sanya guda daga cikin matasan ya rasa ransa inda wasu da dama suka samu raunuka da dama.