Labarai
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar dan kasar Lebanon da sace
Rundunar ‘yan sandan jihar kano ta tabbatar da mutuwar Dan Kasar Lebanon din nan da masu garkuwa da mutane suka sace lokacin da suke tsaka da gudanar da aikin gadar shataletan Dangi ranar Talatar da ta gabata.
Kakakin Rundunar Yan’sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya tabbatarwa manema labarai cewa an tsinci gawarsa ne a kan titin zuwa Maiduguri a daren jiya Alhamis.
DSP Abdullahi Haruna ya kuma kara da cewa tuni suka mika gawar zuwa Asibitin kwararru na Murtala Muhammad domin gano Musabbabin mutuwar tasa.
Rahotanin sun bayyana cewar tuni iyalan mammacin suka samu labari kuma har sun fara shirye-shiryen mayar da gawar zuwa kasar su.
A ranar Talatar da ta gabata ne dai wasu ‘yan nindiga da ba a san ko suwaye ba suka bude wa ma’aikatan dake aiki a gadar shataletalen Dangi wuta, yayin da suka sace mutumin, nan take kuma suka kashe direban sa.