Labarai
Rundunar ‘yan sanda zata aika jirage yankunan da ake rikici
Sufeto Janar na ‘yan sandan Nageriya Muhammad Adamu, ya ba da umarnin turawa da jirage masu saukar ungulu na rundunar a sassan kasar baki daya domin dakile matsalolin tsaro.
Rahotanni sun ce, jiragen na shalkwabta zasu gudanar da aiki a sassan kudu maso yammaci da kuma arewa maso yammacin kasar .
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran rundunar, DCP Frank Mba.
Sanarwar ta ce jiragen masu saukar ungulu zasu rika kula da harkokin tsaro a yankunan arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammaci wanda nan ne aka fi samun matsalolin ayyukan batagari a wannan lokacin.
A cewar sanarwar, akwai cibiya a Abuja da za ta rika kula da titin Kaduna zuwa Abuja da kuma sauran jihohi da ke yankunan arewa maso tsakiya da arewa maso yamma, sai kuma cibiyar da ke jihar Ondo wadda za ta rika kula da jihohin kudu maso yammci.