Labarai
Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce ta tarwatsa wasu gungun ‘yan fashi a jihar

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta ce tarwatsa wani gungun matasa da suka addabi al’ummar unguwannin Medile da Guringawa da fashi da makami.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, inda ya ce matasan suna amfani da makamai wajen haurawa gidajen jama’a suna yi musu fashi.
Bayanai sun nuna cewa bata garin suna balle kofofin gidaje tare da tsorata masu gida da wukake, inda suke kwashe baburan hawa da wayoyi da kuma kudade, har ma su raunata wasu.
CSP Kiyawa ya kara da cewa an samu nasarar ne da tallafin ‘yan kwamitin tsaro na unguwa, kuma tuni aka gurfanar da wasu daga cikinsu a gaban kotu wacce ta aike da su gidan gyaran hali.
You must be logged in to post a comment Login