Labarai
Rundunar Yan sandan Kano ta karbi bindigogi da albarusai 60 da mutanen ke rike da su ba bisa kaida ba suka mika mata
Rundunar Yansanda ta jahar Kano ta karbi bindigogi da albarusai guda 60 daga hannun mutane da suka mika da kansu domin yin biyayya ga umarnin babban sufeton Yan sanda Ibrahim Idris.
Kwamishinan Yan sanda na Jihar Kano Rabiu Yusuf ne ya bayyana hakan ga manema labarai a matakin da rundunar ta dauka nakira ga mutane su mika makaman dake hannunusu da su ka mallaka ba bisa kaida ba.
Yace bindigogin da albarusan da aka mika yau an samo su ne daga hannun mutane da suka bi umaranin mika makamai da suka mallaka ba bisa kaida ba.
Kwamiuhinan Yanasanda Rabiu Yusuf yace mika makaman hanya ce ta kawar da makamai da jamaa suka mallaka ba bisa kaida ba kafin zaben 2019.
Rabiu Yusuf ya kuma gargadi cewa duk wanda yaki ya mika makaman da ya mualaka ba bisa kaida ba kuma aka kamashi doka zata yi aiki a kansa.