Kiwon Lafiya
rundunar yansandan kano ta musanta cewa jami’anta sun yi harbi mutane a Ado Bayero Mall
Rundunar ‘yansanda Kano ta ce babu kanshin gaskiya a rahotannin da wata kafar yada labarai ta ruwaito cewa jami’anta da ke kula da rukunin kantunan Ado Bayero anan birnin Kano sun harbe mutane hudu a shekaran jiya Lahadi.
Mai magana da yawun rundunar SP Magaji Musa Majiya ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai da safiyar Talatar nan.
Cikin sanarwar dai Magaji Musa Majiya, ya ce; rahoton da kafar sadarwa ta Solacebase ta ruwaito cewa ‘yansanda sun harbe mutane hudu sakamakon cunkoso da aka samu biyo bayan yawan jama’a da ke neman shiga rukunin kantunan na Ado Bayero da ke titin zoo ba gaskiya bane.
A Lahadin da ta gabata ne dai rahotanni su ka bayyana cewa, wasu jami’an ‘yansanda da ke kula da rukunin kantunan Ado Bayero da ke titin Zoo suka harbe mutane hudu a lokacin da suke yunkurin shiga rukunin kantunan don yin sayayya da kallon wasanni sallah da ake gudanarwa a harabar.
Malam Yusuf Adamu yana daya daga cikin wadanda tsautsayin ya ritsa da su yana kuma karbar magani a asibiti ya kuma shaidawa wakilin cewa yana kan hanyarsa ta zuwa gida ne akan titin da Ado Bayero Mall din yake inda wurin ya cika makil da masu son shiga ciki wanda dandazon jama’ar ne ya sanya ‘yan sandan ke korar mutane suna komawa kuma hakan ce ta sanya ‘yan sandan yin harbi inda suka same shi a cinya sai kuma karin wasu mutum 3 da ya ce an kawo su asibiti mutum daya harbin ya same shi a hannu da wani kuma da aka same shi a kirji.