Labarai
Rushe gidan mari na Kano ya kara haifar da koma baya – Maigida Kachako
DAGA: SAFARA’U TIJJANI ADAM
Kwamitin hadin guiwa da killace masu shaye shaye na jihar kano ya bayyana takicinsa kan rushe gidajen mari a Kano.
Kwamitin ya bukaci gwamnatin jihar ta kara samar da cibiyoyin da za’a rika rika killace masu shaye-shaye don basu tarbiyya da kuma kawo karshen masu tu’ammali da kwayoyin maye a jihar.
Shugaban kwamiti Malam Yakubu Maigida Kachako ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin ”Barka da Hantsi’’na nan tashar Freedom da shirin ya mayar da hankali kan matsalar shaye shaye.
Maigida Kachako ya kuma ce kamata yayi iyaye su rika zuwa cibiyoyin da ake killace masu tu’ammali da kwaya musamman ma iyayen da yaransu suke shaye-shayen domin samun nutsuwar yaran.
Ya ce rushe gidan mari da aka yi ya kara haifar da yawaitar masu shaye-shaye a Kano, wanda har kawo yanzu an gaza shawo kan su.
You must be logged in to post a comment Login