Labarai
Ruwan sama ya yi sanadiyyar lalata amfanin gona a Kano
Mamakon ruwan sama da aka yi a karamar hukumar Bagwai ya lalata amfanin gona da ya tasamma na Naira milyan 40.
Mataimakin shugaban karamar hukumar ta Bagwai Aminu Ibrahim Gogori ne ya shaidawa jaridar Kano Focus hakan cikin makon da ya gabata.
Ibrahim Gogori ya ce yankunan da ibtila’in yafi shafa sun hada da Gadanya da Gadanya Gabas da Jobe Tsauwa da Tsattawa da kuma Galawa.
Ya kara da cewa fiye da manoma 445 ne suka yi asarar amfanin gonar su a yayin mamakon ruwan.
Mataimakin shugaban karamar hukumar ya ce tuni hukumomin wannan yanki suka shiga duba irin asarar da wadannan manoma suka yi don daukar mataki na gaba.
Shima a nasa bangaren Dagacin Gadanya Shuaibu Abubakar da takwaransa na Jobe Abdullahi Lawal, sun bukaci Gwamnatin tarayya da ta kawo musu dauki.
Ko da aka tuntubi shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano Sale Aliyu Jili ya nuna rashin jin dadin sa, inda ya bukaci hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA ta shigo don tallafa wanda ibtila’in ya shafa a jihar.
You must be logged in to post a comment Login