Labaran Kano
Saɓa ƙa’ida: An rufe kamfanoni 4 na ƴan China a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wasu kamfano 4 mallakin ƴan kasar China da ke sarrafa ledar da aka yi amfani da ita.
An rufe kamfanin sakamakon zarginsu da gudanar da aiki ba bisa ƙa’ida ba.
Jami’in kula da harkokin kasuwanci na ma’aikatar masana’antu da kasuwanci ta jihar Kano Adamu Umar ne ya jagoranci gudanar da rufe kamfanonin.
Da yake jawabi ga manema labarai mataimakin shugaban kungiyar Kwadago ta ƙasa NLC reshen jihar Kano Kwamared Ado Salisu Riruwai ya ce “kamata ya yi a ce ƴan asalin Jihar Kano ne suka mallaki irin waɗannan kamfanoni”.
A na sa bangaren shugaban kungiyar masu sana’ar tara robobi da kwalaye da aka yi amfani da su Kwamared Salisu Ali Yarima ya yabawa matakin gwamnati na rufe kamfanonin.
“matakin da gwamnatin jihar Kano ta ɗauka na rufe kamfanonin ƴan China zai ba da dama ga ƴan kasa su kafa nasu tare da bunƙasa tattalin arziki.
You must be logged in to post a comment Login