Labarai
Sabo da Kaza: Ba sani ba sabo ga wanda muka samu da rashawa – Muhyi Magaji
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta jaddada aniyarta na ci gaba da bibiyar hakkin al’umma tare da daukan hukunci akan duk mai laifi.
Shugaban hukumar Muhyi Magaji Rimin-Gado ne ya bayyana hakan, yayin da yake jawabi a taron karawa juna sani da hukumar ta shirya kan hanyoyin da za abi wajen magance laifukan cin hanci da rashawa a jihar Kano dama kasa baki daya.
Ya ce, hukumar a shirye take ta karbi kowane korafi na al’umma dangane da kwato musu hakkinsu ba tare da karbar ko sisi a hannun al’umma ba.
A nasa jawabin Kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista Musa Abdullahi Lawan, ya ce, za su yi aiki kafada da kafada da hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da rashawa don ganin an magance laifukan cin hanci a jihar Kano.
Wakilin mu Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa, hukumomi da dama ne suka hallarcin taron na yau da suka hada da EFCC da ma’aikatan Kotu da kuma kungiyoyin rajin kare hakkin Dan Adam.
You must be logged in to post a comment Login