Labaran Kano
Wani Sabon gidan abincin Naira Talatin ya hana wasu Almajirai bara a Kano.
A unguwar Sani Mainagge,sakamakon sake bude gidan abinci na Naira talatin gidaje dake makwabtaka da gurin sun fara sauke tukwanansu.
Biyo bayan maganar da minstan noma Alhaji Sabo Nanono yayi, a game da abincin Naira talatin ,wanda sakamakon hakan ya saka aka bude gidan abincin a unguwar Sani Mai Nagge.
Sai ga shi wani mai gyaran Rediyo ya samu karfin giwa inda shi ma ya bude gidan abincin na Naira 30.
Wanda ya bude gidan ya shaidawa Freedom Radio cewa sakamakon bude gidan abincin na Naira talatin makotansa sun sauke tukwane saboda saukin abincin sa.
Haruna Injinya ya kara da cewa makotan nasa kan turo yara biyar da Naira dari da hamsin domin sayan abinci.
Haruna mai sabon gidan abincin na Naira 30 ya kara da cewa a rana yana dafa shinkafa buhu daya da wake rabin buhu da garin kwaki buhu daya.
Ya kara da cewa wasu na zuwa gidan abincin domin saye a rabawa mabukata.
A nata bangaren mai dakin da ya bude sabon gidan abincin Hajiya Sadiya Saidu ,ta ce hatta Almajiran unguwar na zuwa sayan abincin na Naira talatin.
Ta kara da cewa hakan ta sa Almajiran sun daina bara sai dai su nemo Naira talatin domin sayan abincin.