Labarai
Sabon Kwamishina ya umarci ‘yan sandan Kano su kauce wa karabar cin Hanci
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Muhammad Usaini Gumel ya gargadi jami’an rundunar da su kauce wa aikata duk wani laifin karbar cin hanci da rashawa domin ko kadan bazai lamunci abunda zai batawa ‘yan sanda suna ba.
Kwamishinan, ya bayyana hakan ne yau Talata lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan fara kama aiki da ya yi a matsayin sabon kwamishinan ‘yan sanda.
Muhammad Usaini Gumel ya kara da cewa rundunar ‘yan sandan Jihar Kano za ta rika amfani da sabbin dabaru na zamani wajen cafke duk wasu masu aikata muggan laifuka a fadin jihar Kano domin tabbatarda tsaro da zaman lafiya.
Ya kuma bukaci hadin kan sauran hukumomin tsaro da kungiyoyin al’umma da kuma ‘yan sandan cikin al’umma da su ci gaba da bai wa rundunar yan sandan hadin kai domin magance matsalar tabarbarewar tsaro.
You must be logged in to post a comment Login