Labarai
Sabon rikici ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 40 a Sudan ta Kudu
Kimanin mutane 45 ne suka rasa rayukansu a yayin wasu rikice-rikice na kabilanci a kasar Sudan ta Kudu, in ji hukumomin kasar.
Akalla mutane 18 suka jikkata lokacin da wasu mayaka dauke da makamai daga kabilar Atok Buk suka kaiwa wasu garuruwa na kabilar Apuk Parek da ke gundumar Tonj ta Arewa a jihar Warrap.
A cewar kwamishina mai wakiltar gundumar, Andrew Deng, an kona kauyuka da dama a harin, yayin da dubunnan mazauna garin suka tsere daga yankin.
Mahukuntan yankin sun yi ittifakin cewa harin ramuwar gayya ce ga hare-haren da suka faru makonni da suka gabata.
Rikice-rikicen kabilanci sun jima sun a faruwa tsakanin kabilu a cikin Sudan da ke gabashin Afirka.
A hare-hare da ake yi akwai batu na satar shanu da kuma satar yara a wasu lokuta inda ake amfani da su a matsayin bayi.
A farkon watan Yuni, Kwamitin kasa da kasa na kungiyar ba da agaji ta Red Cross ya yi gargadin cewa harin masu dauke da makamai da ke haifar da asarar rayuka da rashin matsugunni na kara Kamari a yankuna daban-daban na Sudan ta Kudu.
You must be logged in to post a comment Login