Labarai
Safarar kwayoyin maye: Mun kama sama da mutane dubu 8 a watanni 8 – Buba Marwa
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ce, ta kama sama da mutane dubu 8 da 634 da suka yo safarar miyagun kwayoyi daga farkon shekarar da muke ciki zuwa Agustan da ya gabata.
Shugaban hukumar Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ne ya bayyana hakan a wnai taro da ya gudanar.
Marwa ya shaidawa kungiyoyin kare hakkin dan adam da ma’aikatar jin kai da ci gaban al’umma har ma da kwamitin majalisar dinkin duniya cewa, NDLEA ta kama kwayoyin maye da kudin su ya sama da bliyan 100 a tsakanin watannin.
Buba Marwa ya kuma ce, annobar corona ta taka rawa wajen karuwar laifukan safarar kwayoyin maye a fadin duniya.
You must be logged in to post a comment Login