Kiwon Lafiya
Laminu Sani:yancin kai ga kananan hukumomi zai taimaka wajen raya kasa
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi ALGON reshen Jihar Kano kuma shugaban karamar hukumar Nassarawa Alhaji Laminu Sani, ya bayyana cewa sahalewa kananan hukumomi ‘yancin gashin kai abu ne da zai taimakawa kananan hukumomin wajen samar da ayyukan raya kasa.
Alhaji Lamin Sani, ya bayyana hakan ne a jiya ta cikin shirin Mu Leka Mu Gano na musamman na nan tashar Freedom Rediyo.
Ya ce abu ne mai matukar muhimmanci baiwa kananan hukumomi damar cin gashin kai don samar da ayyukan ci-gaba a yankunansu tare da sanya musu ido kan yadda za su kashe kudaden da aka ba su don gudun barnatar da su.
Haka zalika ya ce abinda kungiyar ta su ta sanya a gaba shi ne, bin hanyoyin da za su ciyar da kananan hukumomin Jihar Kano gaba.
Alhaji Laminu Sani, ya kuma ce matsalar karancin kudi da ake fama da shi a kananan hukumomi, hakan ba zai sanya su gajiya ba wajen samarwa da matasa aikin yi da sauran ayyukan da za su ciyar da al’umma gaba.