Labarai
Sai da binciken kwakwaf za’a shawo kan matsalar cin hanci -Anas Aremauyaw
Aikin jarida na binciken kwa-kwaf wani babban makami ne wajen yake da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Kwararren dan jaridar nan kuma wanda ya karbi kyaututtuka da dama kan kwarewar sa dan asalin kasar Ghana Anas Aremayaw ya ce, aikin jarida na binciken kwa-kwaf wani babban makami ne wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Haka zalika Anas yace rahoton bincikar kwa-kwaf wani makami ne na yaki tare da shawo kan matsalolin cin hanci da rashawa a kasar nan, da ma nahiyar Afrika baki daya.
Anas Aremeyew ya bayyana hakan ne a yayin bude taron karawa juna sani na kwanaki biyu ga masu aikin jarida na binciken kwa-kwaf na nan gida Najeriya da kuma kasar Ghana da malamai da dalibai masu nazari a jami’o’I da kwalejojin ilimi da kimiyya da fasaha wanda aka yi a harabar jami’ar Bayero dake nan Kano a yau Alhamis.
Da yake jawabi kan yadda yake tattara bayanai wajen hada rahoton fallasa ko bankada masu cin hanci da rashawa, Anas yace akwai kalubale daban-daban da yake fuskanta, amma hakan bai kashe masa gwiwa ba, a don haka ya bukaci ‘yan jarida da dalibai masu nazari da su dinga bincikar kwakwaf wajen yin rahotannin kwarmata masu cin hanci da rashawa a cikin alumma.
A yayin da dalibai ke masa tambayoyi kan yadda yake rufe fuskar sa don kada a gane shi a cikin alumma, dan jaridar ya ce wata alama ce da yake amfani da shi don kare kan sa, yayin da ya bukaci makarantu da jami’o’I a kasashen Afrika da su sanya nazari kan ilimin binciken kwa-kwaf na jarida a tsarin manhajar su, a wani mataki na karfafawa dalibai yin rahoton bincike kan cin hanci da rashawa.
Da yake jawabi fitaccen dan jaridar nan kuma tsohon babban sakatare a ma’aikatar yada labarai, Ahmad Aminu yace yawancin ‘yan jaridar yanzu sun sanya tsoro a zukantan su, a don haka ya bukace su da su sake jajircewa wajen gudanar da ayyukan su yadda ya kamata, mussaman ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.