Labarai
Sakon Sallah: NUJ Reshen Freedom Radio ta taya Musulmi murna
Kungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya NUJ, reshen gidan Rediyon Freedom da ke jihar Kano, taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin Sallah ta bana.
Hakan na cikin sanarwar da kungiyar ta fitar mai dauke da sa hannun shugaba Aisha Muhammad Yalleman da Sakatarenta Muzammil Ibrahim Yakasai.
Kungiyar ta bukaci al’ummar musulmi da su kara himma, ta hanyar sadaukarwa ga juna da nuna kauna da kulawa da jin-kai da taimakon ma bukata tare rubanya ayyukan alheri da ci gaba da addu’ar zaman lafiya ga kasa baki daya.
Har ila yau, Kungiyar ta bukaci, ma’aikatan yada labarai da su bi ka’idojin aikin yayin da suke gudanar da aikinsu.
NUJ ɗin reshen Freedom Radio, ta yi kira ga sabbin shugabannin da za a rantsar nan ba da dadewa ba, da su sanya Nijeriya a gaba, da kuma tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta, ta fuskar zamantakewar da siyasa da harkokin tattalin arziki da rashin tsaro musamman wajen magance matsalar masu kwacen wayoyin salula.
Haka kuma kungiyar, ta yi addu’ar fatan al’ummar musulmi za su gudanar da bukukuwan karamar Sallah lafiya.
You must be logged in to post a comment Login