Connect with us

Labarai

Masarautar Kano ta dakatar da Hawan Dawakai yayin bikin Sallah

Published

on

Majalisar masarautar kano ta sanar da janyewa daga dukkan shirye-shiryen gudanar haye-hayen bikin babbar sallah na bana.
‎
‎Masarautar Kano ta bayyana hakan ne ta bakin babban ɗan majalissar Sarki kuma Matawallen Kano Alhaji Aliyu Ibrahim.
‎
‎Ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne bayan samun shawarwari daga jami’an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar Kano yayin bukukuwan Sallah.
‎
‎Matakin na zuwa ne bayan Rundunar Ƴan sandan Kano ta sanar da dakatar da duk wasu harkokin hawan Sallah saboda dalilan tsaro.
‎
‎A baya dai ana sa ran Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu zai gudanar da hawan Daushe tare da hakimai da sauran mahaya yau Alhamis kafin sanar da janye hawan.
‎

Matawallen Kano Alhaji Aliyu Ibrahim, ya bukaci daukacin al’umma da suyi hakuri tare da gudanar da adduoi na musamman don samun dorewar zaman lafiya a jihar nan dama kasa baki daya.
‎

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!