Connect with us

Addini

Sallar bana ba laifi sai dai muna fama da matsalar tsadar kayan aiki – teloli.

Published

on

Sana’ar dinki na daya daga cikin sana’o’i da matasa ke yi a fadin duniya, wadda a wannan lokaci na watan Ramadan aka fi yin ta fiya da sauran watanni domin tunkarar hidindimun salla.

 

Kasancewar sallah na karatowa, ya sa muka tuntubi wasu teloli don jin shin ya abin yake a bana, wadanda wasunsu suka bayyana cewa sukam a bana ba yabo ba fallasa domin kuwa kasuwa ta yi kyau.

 

A cewar telolin sana’ar dinki a bana tana tafiya kamar yadda ya kamata kuma suna cin kasuwa, sai dai suna fama da matsalar tsadar kayan dinki.

 

Telolin sun kuma ce a bana ba za su yi halin nan da ake zarginsu da yi ba na rashin cika alkawari.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!