Kiwon Lafiya
Sama da mutum 2,000 ne suka amfana da kayan masarufi na azumi da Hajiya Halima Shekarau ta raba
Uwar gidan tsohon ministan ilimin kasar nan Hajiya Halima Ibrahim Shekarau, ta yi kira ga masu hali da su tallafa wa nakasassu da marasa karfi da kayan abincin da zasu yi amfani da shi a cikin Azumin watan Ramadana da ke karatowa.
Hajiya Halima Ibrahim Shekarau ta bayyana hakan ne yayin da take rabon tallafin kayan abinci ga nakasassu da marasa karfi wanda ya gudana yau a nan Kano.
Ta ce kasancewar akwai dimbin mabukata a cikin al’umma, don haka akwai bukatar a tallafa wa marasa karfi da kayan masarufi da nufin saukaka musu matsanancin rashin da suke fama da shi.
wasu daga cikin makafi da guragu da kuma iyayen marayu da suka amfana da tallafin sun bayyana yadda suka ji kan kayan da aka basu inda har ma wasu daga ciki suka bayyana cewa dama sun saba zuwa suna karbar tallafi a wajenta, har ma suka yi mata fatan alheri.
Fiye da mabukata mutum 2,000 ne dai suka amfana da rabon kayan masarufin da suka hadar da Shinkafa da Gero Sukari da sauran kayan masarufi.