Connect with us

Labarai

Sama da shekara 20 mahaifina ke safarar ƙwayoyi – Matashi

Published

on

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta cafke wani matashi Kabiru Muhammad a unguwar Ɗanbare ɗauke da sinƙi-sinƙin tabar wiwi 49.

An sarrafa tabar ne tamkar sinƙin Biredi.

Matashin mai shekara 21 ya ce, wiwin ta mahaifinsa ce, kuma yanzu an kama shi, hakan ya sa mahaifiyarsa ta umarce shi da ya sauya wa tabar wuri.

A cewar sa, mahaifin na sa ya shafe sama da shekara ashirin yana sana’ar safarar tabar wiwin.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce, sun cafke matashin ne ta hanyar bayanan sirri da suka samu.

Kiyawa ya ce, tuni aka mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ƴan sandan Kano.

Labarai masu alaka:

Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya kai tallafi ga ‘yan gudun hijira

Kano: Majalisar wakilai ta nemi a rushe ƴan sandan ‘Anti Daba’

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!