Labaran Kano
Samar da lantarki mai amfani da hasken rana ne kadai zai magance tashin gobara a kasuwanni
Shugaban kasuwar Muhammad Abubakar Rimi wato sabon gari dake Kano Alha Uba Zubairu Yakasai ya ce amfani da lantarki na haske rana ce kadai hanyar da zata magance matsalar gobara da ake yawan samu wanda ke haddasa asara da dama.
Alh Zubairu ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai da aka gudanar yau a offishin kungiyar yan jaridu dake kano.
Ya jaddada cewar sanya lantarki mai amfani da hasken rana ce kadai zai magance matsalolin da yan kasuwa ke fuskanta musammam ma matsaloli da suka shafi yawan tashin gobora da ake samu wanda ke haddasa asarar dukiyoyi da dama.
Ya ce tsarin samar da lantarki mai amfani da hasken rana na daga cikin tsare-tsaren da gwamatin tarayya ta fito da shi a wasu daga cikin kasuwannin da ke fadin kasar.
Ya bukaci ‘yan kasuwa da su marawa gwamnatin tarayya baya dangane da wannan yunkuri nata na samar da lantarki mai amfani da hasken rana don magance matsala ta gobora.
Alh Zubairu ya bukaci shugabannin da ke aikin samar da wutar lantarkin ta hanyar amfani da hasken rana da su rage farashin da suke shirin bayarwa domin saukakawa ‘yan kasuwa.
A cewar sa samar da wutar lantarki da wani kamfani ke ba su wanda ake yi wa lakabi da merger na daga cikin dalilan da ya sa wasu ‘yan kasuwa suka ki karbar lantarki mai amfani da hasken rana