Labarai
Samun ƴancin kai ya kawo ci gaba a ɓngaren shari’a – Babajibo Ibrahim
Mai magana da yawun kotunan jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya ce, bayan samun ƴancin kai daga turawan mulkin mallaka na Burtaniya Alkalai suma sun samu ƴancin kan su.
A cewar sa tun bayan samun ƴancin kan Ademola shi ne Alƙali na farko ɗan ƙasa daya fara yin sugabanci lauyoyi a kasar na.
Babajibo Ibrahim ya ce, a wancan lokacin karatun lauya sai an je can ƙasashen ƙetare sannan ake yinsa .
“A nan kano ma haka abin yake turawan ke rike da bangaren shari’a sai kuma daga baya aka samar da hukumar shari’a da rukunin kotuna na jihar kano” a cewar Babajibo.
Ya kuma ce an samar da ɓangaren harkokin shari’a a 1968 wanda chif joji na farko shi ne justice Dahiru Mustapha har sai da ya riƙe kotun koli ta tarayya kafin Allah ya yi masa rasuwa .
“Ci gaban da aka samu a yanzu a ɓangaren shari’a a yanzu shi ne samuwar kotuna acikin mutane wanda hakan ne ya samarwa mutane sauki da kuma ƙarin alƙalai sabanin wancan lokacin Kano da Jigawa kotuna basu fi 4 ba Kuma ana shan wahala kafin jama’a su kai korafin su”. in ji Babajibo.
You must be logged in to post a comment Login