Labarai
Sana’ar Achaba ta dawo Kano gadan-gadan
Sana’ar babur mai ƙafa biyu ta dawo jihar Kano gadan-gadan a wannan lokaci da ake tsaka da yajin aikin matuƙa baburan adaidaita.
Tun bayan da masu baburan Adaidaitar suka tsunduma yajin aiki, al’ummomi da dama ke fuskantar matsalar ababen hawa, musamman ɗalibai da masu zuwa kasuwanni tare da ma’aikatan da ke fita wuraren ayyuka.
To sai dai ana iya cewa yajin aikin na ƴan Adaidaita Sahu, ya buɗewa masu babur mai ƙafa biyu ƙofa wajen shigowa gari domin ragewa jama’a raɗaɗin rashin masu adaidaita sahun, kamar yadda wasu masu babur mai kafa biyun su ka shaida wa Freedom Radio.
Mutane da dama ne dai suka shiga tsaka mai wuya saboda rashin samun baburan na adaidaita sahu, to sai dai wasu da muka zanta da su sun ce sunyi farin ciki da ganin ƴan Acaɓa na zirga-zirgar daukar mutane, duk kuwa da cewa tun a lokacin gwamnatin baya aka haramta amfani dasu.
Sai dai mafi yawa daga cikin mutanen sun nuna rashin jin daɗinsu na rashin adaidaita sahu sakamakon ba kowa ke iya hawa babur mai ƙafa biyu a cikin gari ba.
You must be logged in to post a comment Login