Labarai
Sanata Ahmad Lawan ya musanta zargin jagorantar gyara ga kundin tsarin mulkin kasa
‘Yan majalisar dattawa da ke goyon bayan shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Ahmed Lawan sun musanta cewa, Sanata Ahmed Lawan idan ya samu nasarar zama shugaban majalisar zai jagoranci gyara ga kundin tsarin mulkin kasar nan don bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari zarcewa karo na uku.
Mai magana da yawun kungiyar Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.
Sanarwar ta ce ya zama wajibi su mayar da martani kan labaran da aka yada cewa Sanata Ahmed Lawan zai jagoranci yin gyara ga kundin tsarin mulkin kasar nan don baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari damar zarcewa karo na uku, idan wa’adin mulkin sa ya kare.
A cewar sa wasu ‘yan siyasa ne kawai da ke da burin jagorantar majalisar suka kitsa maganar da nufin zubar da kimar Sanata Ahmed Lawan.
Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya kuma ce lokacin da Sanatoci ‘yan jam’iyyar APC suka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kwanaki uku da suka gabata, ya shaida musu cewa ya tsaya takarar shugaban kasa har sau biyar kuma wannan shine na karshen da yayi.