Connect with us

Labarai

Kamfanin NNPC ya rufe karbar masu neman aiki a hukumar a jiya

Published

on

Kamfanin mai na kasa NNPC ya rufe karbar rajistar masu neman aiki a hukumar a jiya Laraba tare da fara tantance wadanda suka fi cancanta.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun  hukumar Mr Ndu Ughamadu ya fitar jiya a Abuja.

Sanarwar ta ce kamfanin ya kammala tattara kididdigar wadanda su ka yi rajista don neman aiki a kamfanin na NNPC, abinda ya rage yanzu shine fara tantance su don zabar wadanda suka fi cancanta.

Ndu Ughamadu ta cikin sanarwar dai ya kuma ce wadanda aka tantance kuma suka fi cancanta za a gayyace su don rubuta jarabawar gwajin kwazonsu wato Aptitude test.

A cewar sanarwar za a gudanar da jarabawar gwajin kwazon ne a cibiyoyi hamsin da ke kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,890 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!