Labarai
Sanata Barau Jibrin da Ganduje sun Isa Saudiyya halartar jana’izar Aminu Dantata

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, tare da tsohon Shugaban jam’iyyar APC Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sun sauka a birnin Madina, domin halartar jana’izar, Alhaji Aminu Dantata.
Tun a cikin daren jiya Litinin ne wata sanarwa da mai bai wa Sanata Barau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar ta bayyana cewa, jiga-jigan na jam’iyyar APC sun bar gida Najeriya inda suka kama hanyar zuwa jana’izar.
Mataimakin shugaban majalisar Dattawan, Barau Jibril da Ganduje sun samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano Alhaji Abdullahi Abbas da shugaban kwamitin Dattawa kan manyan makarantu Sanata Muntari Dandutse sai Ali Madaki.
Tawagar ta tashi daga Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
You must be logged in to post a comment Login