Labarai
Sannu a hankali sojojin kasar nan na samun galaba – Majalisa
Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan, ya ce sannu a hankali sojin kasar nan na samun galaba akan abokan gaba, la’akari da yan da aka samu saukin kai hare-haren ‘yan bindiga a kasar.
Senata Ahmad Lawan, ya bayyana hakan ne lokacin da wata tawagar yan’asalin jihar Adamawa suka kai masa ziyara a Abuja.
Jaridar The Nation ta rawaito, Shugaban majalisar na cewa koda yake akwai tufka da war-wara a sha’anin tsaron kasar nan , to amma muddun jami’an tsaro suka tashi tsaye to kuwa za’a kawo karshen matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta a halin yanzu.
You must be logged in to post a comment Login