Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Sanya tufafin da ke da zallar auduga zai taimaka wajen rage tsananin zafi

Published

on

Wani likita a sashen kula da lafiyar al’umma na Asibitin koyarwar na Aminu Kano da ke nan Kano Dr Mukhtar Gadanya, ya ce, amfani da suturun da aka saka su da Auduga zai taimaka matuka wajen rage tsananin zafin da ake fuskanta musamman a yanzu da aka fara ibadar Azumin watan Ramadana.

Dr Mukhtar Gadanya, ya bayyana hakan ne ta cikin shirin ‘Mu leka Mu Gano’ na musamman na nan Freedom Radio, da ya mayar da hankali kan yadda mutane za su gudanar da Azumi cikin sauki musamman ma masu fama da rashin lafiya.

Ya ce la’akari da irin zafi da ake fama da shi yanzu, akwai bukatar mutane su rika amfani da hanyoyin da za su saukaka musu jin zafin.

Ya kuma shawarci mutane da su kauracewa amfani da ababen sha masu sanyi yayin bude baki domin kiyaye lafiyar su.

Haka kuma ya ce zai fi kyautatuwa a rika amfani da kayan marmari domin inganta lafiyar jiki tare da rage yawan cin abincin da ya wuce kima.

Dr Mukhtar Gadanya, ya kuma bukaci mutane su rika yin Sahur da abinci marasa nauyi ta yadda abincin da suka ci zai narke ba tare da dukar tsawon lokaci ba wanda hakan zai taimaka wa mai Azumi matuka.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!