Labarai
Sarki Aminu Ado Bayero ya nada sababbin Hakimai 6
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya nada sababbin Hakimai guda shida.
Wadanda aka nada din sun hadar da Alhaji Abbas Maje Ado Bayero a matsayin Bauran Kano da Alhaji Kabiru Ado Bayero a matsayin San Turakin Kano da Alhaji Umar Ado Bayero wanda aka nada shi Yariman Kano.
Sauran su ne Alhaji Tijjani Ado Bayero a Matsayin Zannan Kano da Alhaji Auwalu Ado Bayero a Matsayin Sadaukin Kano da Alhaji Ado Ado Bayero a matsayin Cigarin Kano.
Da yake jawabi lokacin da aka nada Hakiman, Mai Martaba Sakin ya ce, masarautar ta nada su sarautun ne bisa cancanta da tare da irin gudunmawar da suke bayarwa a cikin al’umma.
Haka kuma, Sarkin na Kano ya hore su da su sanya halayyar magabatansu na yin koyi da kyawawan halaye wadanda suka hadar da Juriya da hakuri da amana tare da tausayawa talakawa.
Sarki Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kuma umarci sabbin Hakiman da su dauki halayyar magabata ta mika dukkan al’amuransu ga Allah tare da yin biyayya ga wadanda suka taras a cikin tsarin Hakimci da kuma yin da a kamar yadda suka taso suka ga ana yi kasancewarsu dukkanninsu yan gidan sarautar Kano ne.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login