Labarai
Sarki Aminu Ado Bayero ya umarci shugabannin POLAC su rika daukar dalibai masu kwazo
Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya umarci shuwagabanin makarantar horas da yanda sanda da ke garin Wudil da su rika daukar dalibai masu hazaka domin ingantawa tare da tabbatar da tsaro a fadin Nijeriya.
Sarkin ya furta hakan ne lokacin da ya karbi ba kuncin shugabanin gudanarwar makarantar bisa jagorancin sabon Kwamandan makarantar AIG Sadik Abubakar a fadarsa.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce, aikin ‘yan sanda na da matukar mahimmanci duba da yadda ake samun bata gari suna lalata dukiyoyin al’umma.
A nasa jawabin sabon Kwamandan makarantar AIG Sadik Abubakar, ya ce, sun kai ziyara fadar sarkin ne domin yi masa gaisuwar ban-girma tare da gabatar da kansa amatsayin sabon kwamandan makarantar.
Rahoton: Shamsu Da’u Abdullahi
You must be logged in to post a comment Login