Labarai
Sarkin askar Kano ya kalubalanci likitoci akan yi wa maza shayi
Sarkin Askar jihar Kano Ahaji Dakta na Bango ya kalubalanci likitoci akan su daina sukar salon yi wa maza shayi da suke yi su.
Alhaji Dakta na bango ya bayyana hakan ne a yayin da ya kira taron manema Labarai domin nuna takaicinsa kan irin kallon raini da Likitoci suke yiwa sana`arsu.
A cewar sa sun gada ne tun iyaye da kakanni ba wai da rana tsaka kawai suka shiga sana`ar ba.
Ka zalika sarkin Askar ya bayyana bambamcin sana`ar tasu da ta likitoci yana mai buga misali da bambancin Kazar gida da Kazar gidan gona.
Na Bango ya kara da cewa a kasashen da aka cigaba likitan turawa basa sukar masu magugunan gargajiya,ko kuma su kan su masu maganin gargajiya su soki magugunan turawa.
Yana mai cewar akan haka ya zama wajibi likotoci su dena sukar kai tsaye su don kuwa su basa yi.
Sarkin Askar ya kara da fadar bambanci akan shayi,inda yace shayi ya kasu a kalla kala Goma, kuma bambanci sosai a tsakanin Shayin asibiti da na gargajiya.