Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Manyan abubuwa 4 da hudubar da Muhammadu Sunusi II ta kunsa

Published

on

Tsohon sarkin Kano Malam Muhammad Sunusi na II, mai murabus ya gabatar da hudubar Jumma’a a babban masallacin garin Awe  da jihar Nasarawa tare da jagorantar Sallar a yau.

Malam Muhammadu Sunusi na II, da  yake  tare da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i , wanda ya kai masa ziyara a safiyar yau , a gidan da aka killace tsohon sarkin dake karamar hukumar na Awe , a jihar Nassarawa tun bayan da sauke shi daga Karagar Mulki da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar litinin din makon nan.

Malam Muhammadu Sunusi na II, wanda ya dauki kusan Awa guda yana hudubar ,

  1. Ya yi kira ga al’umma dasu ji tsoron Allah tare da Sallama lamuran su gareshi a koda yaushe ba tare shakku ko akasin haka.
  2. Haka zalika daga cikin kunshin hudubar, ta kara jan hankalin mutane , da su karbi kaddara kyakyawa ko akasin ta, a duk yadda ta same su kasancewar dukkanin nasara tana tare da hakuri.
  3. Sarkin, ya rufe hudubar , da kiran al’umma musulmi dasu hada kansu da taimakon junan su , tare da roka musu nasara a dukkan lamuran da suka saka a gaba , cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
  4. Bugu da kari ya yi addu’ar zaman lafiya ga kasar nan sakamakon rikice- -rikicen da ta ke fama dasu.

Wannan dai na zuwa ne  biyo bayan ,umarnin da wata Babbar Kotu ta bayar a Abuja, da safiyar yau na sakin Sarkin daga daurin talala da aka yi masa tare da bashi damar gudanar da rayuwar sa cikin ‘yan cin walwala ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba ko ka’idoji.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!