Connect with us

Labarai

Sarkin Kano Sunusi na II ya kalubalanci aurar da yara mata kanana

Published

on

 

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya yi kakkausar suka kan duk wani nau’i na cin zarafi ga mata da kuma auren ƙananan yara, yana mai jaddada cewa al’ada ba ta ba wa kowa ikon dukan mace ko tauye mata haƙƙinta. 

 

Sarkin ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels, inda ya ce dukkan ’yan Najeriya suna da kariya a ƙarƙashin doka, ba tare da la’akari da al’ada ko yankin da suka fito ba.

 

Sarki sunusi  ya ce yawancin abubuwan da ake jingina wa al’ada a matsayin dalilin cin zarafi, a zahiri sakamakon talauci ne, rashin daidaiton iko tsakanin maza da mata, da kuma gazawar gwamnati wajen samar da muhimman ayyuka. 

 

Game da auren yara, Sarkin ya ce matsalar ta fi fitowa fili a yankunan karkara, inda ’yan mata ke kammala firamare tun suna da kusan shekara 11 ba tare da samun damar zuwa sakandare ko koyon sana’a ba.  

 

Duk da haka, Sarkin ya jaddada cewa dole ne Najeriya ta tsaya kan ƙa’idoji    da doka, yana mai cewa duk wani nau’i na cin zarafi ga mata da yara ba abin yarda ba ne.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!