Labarai
Sarkin Kano ya buƙaci a kafa kotun hukunta masu safarar Kwaya

Mai Martaba sarkin Kano khalifa Muhammadu Sunusi II, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kafa l kotu ta musamman da za ta rika hukunta masu safarar miyagun kwayoyi a jahoyin Najeriya.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya karɓi bakuncin tawagar Shugaban hukumar yaki da Sha da hana fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen karamar hukumar birni karkashin jagorancin Muhammad Sani Bakori a fadar sa.
Khalifa Muhammadu Sunusi ya ce, samar da dokar Mai tsauri da zata ringa hukunta wadanda Suke shigo da kwayoyi da masu sayar da ita a kasar nan zai taimaka wajen rage yawan Samun masu ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Sarkin yayi kira da ‘yan siyasa da su guji karfafawa matasa gwiwa wajen ta’ammali da miyagun kwayoyi domin Samun matasa masu tasowa nagari.
Anasa bangaran shugaban hukumar Mai Kula da karamar hukumar birni Muhammad Sani Bakori yace,ya Zo fadar sarkin Kano ne domin gabatar da kansa da kuma neman tabarraki.
Shugaban Wanda ya bayyana masarautar Kano da cewa tana da mihimmiyar gudunawar da bayarwa a kokarin da ake na yaki da ta ‘ammali da Sha da fatauci na miyagun kwayoyi
sarkin ya yaba wa shugaban hukumar ta kasa NDLEA Buba marwa bisa kokarin da yake wajen magance matsalar safarar miyagun kwayoyi a kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login