Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna Ganduje ya umarci Limamai su yi huduba kan muhimmancin zaman lafiya yayin zabe

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci Limamain Masallatan Juma’a a fadin jihar da su gudanar da hudubarsu a kan muhimmancin zaman lafiya kafin, yayin da Kuma bayan zaben bana.

Gwamnan ya furta hakan ne da safiyar yau Alhamis yayin ganawarsa da Kungiyar Majalisar Limaman jihar karkashin Jagorancin Limamain masallacin Juma’a na Sheik Ahmad Tijjani da ke Kofar mata Malam Sheik Nasir Muhammad Adam.

Ganduje, ya kuma ce, akwai addu’oin da za a ci gaba da yi don ci gaba da samun zaman lafiya.

Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Ganduje ya kuma umarci komishinan Harkokin Addinai na Jihar Kano Malam Nazifi Muhammad Bichi, ya rubuto buƙatun Majalisar Limamain don daukar matakin da ya kamata.

A nasa jawabin Shugaban Majalisar Limamain ta jihar Kano Sheik Muhammad Nasir Adam, cewa ya yi akwai matsalolin da suka hana Majalisar gudanar da wasu ayyuka da za su kara Inganta ayyukan Limamai.

 

Rahoton: Abba Isah Muhammad

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!