Labarai
Sarkin Kano ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi wanda ya rasu a satin daya gabata.
Sarkin ya bayyana rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi a matsayin babban rashi ba wai kawai ga iyalan sa kadai ba har ma ga daukacin al’ummar musulmi gaba daya.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya ce rasuwar ta bar gibi babba da zai yi wahala a cike duba da irin gudummawar da Shehin Malamin ya bayar wajen hade kan al’umma da bunkasa addinin Musulunci.
A nasa jawabin babban ɗan marigayin Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, ya yi godiya ga Sarkin bisa ta’aziyyar tare da yi wa Sarkin addu’ar samun nasara da jagoranci cikin adalci.
Wakilin mu na masarautar Kano Shamsu Dau Abdullahi, ya rawaito cewa Sarkin na tare da rakiyar manyan hakimai na masarautar Kano da suka hada da wazirin Kano Alhaji Sa’adu Shehu Gidado, Galadiman Kano Alhaji Mannir Sanusi, da Madakin Kano Alhaji Yusif Nabahani Cigari da Kuma manyan jigajigan darikar Tijjaniyya na nan Kano.
You must be logged in to post a comment Login