Kasuwanci
Sarkin Kano ya shawarci al’umma su karbi rancen CBN
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya shawarci kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da masana’antu da su shiga cikin shirin babban bankin Najeriya na bada bashin da babu ruwa a cikinsa da nufin bunkasar kasuwanci da masana’antun jihar Kano.
Alhaji Aminu Ado Bayero, ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da bikin bada tallafin bashi wanda babu kudin ruwa a ciki wanda babban bankin kasa CBN ya shirya a Kofar Kudu da ke gidan sarkin Kano.
Sarkin ya bukaci al’umma da su rungumi wannan shiri na babban bankin Najeriya da nufin habbana sana’ao’insu
A nasa jawabin shugaban hukumar daraktoci na rukunin tashoshin Freedom Radio Alhaji Ado Muhammad, ya kalubalanci masu gudanar da sana’o’in hannu da su rungumi shirin da nufin bunkasar sana’o’in nasu da kuma kananan masana’antu.
Da yake nasa jawabin, shugaban kungiyar masu gudanar da sana’ar tuka baburan adaidaita sahu Alahji Sani Sa’idu Dankoli, ya ce, kungiyarsa ta yi na’am da shirin kuma za ta bashi cikakken goyon baya.
Shi ma shugaban kungiyar manoma ta jihar Kano malam Faruk Rabi’u Mudi, cewa ya yi kungiyarsa ta yi farin ciki da samar da bashin marar kudin ruwa.
Wakilinmu Muhammad Harisu Kofar Nassarawa, ya ruwaito cewa dimbin al’umma ne suka halarci bikin bude shirin na bada tallafin bashin kudin marar ruwa da suka hadar da maza da mata.
You must be logged in to post a comment Login