Labarai
Sarkin Kano zai fitar da mahaddatan alkur’ani karatu kasar waje
Maimartaba Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II ya kai zayara jami’ar Alkasimia dake garin Sharja a hadaddiyar daular larabawa, domin nemawa matasa mahaddata alkur’ani na jihar Kano guraben karatu a makarantar.
A jawabin da maimartaba Sarkin ya gabatar a yayin ziyarar ya bayyana cewa “Muna da makarantu da mahaddata alkur’ani a Najeriya musamman a jihar Kano wadanda za su iya bayar da gagarumar gudummuwa a bangaren alkur’ani da harshen larabci idan suka samu gurbin karatu a wannan jami’a ta Alkasimia.”
Wata majiya daga masarautar Kano ta shaidawa Freedom Radio cewa Sarki Muhammadu Sanusi II ya gana da shugaban makarantar Dakta Rashad Mohammed Salem da kuma sauran jami’anta, inda suka nuna jin dadinsu da ziyarar da sarkin ya kai musu.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Sarkin yayi wata hobbasa wajen bunkasa rayuwar al’umma ba, domin kuwa idan zaku iya tunawa ko a kwanakin baya sarki Muhammadu Sanusi II ya jagoranci kulla alaka da masu zuba hannun jari na kasar Sin, don bunkasa tattalin arzikin jihar Kano, biyo bayan ziyarar da ya kai kasar ta sin.
Haka kuma Sarki Muhammadu Sanusi II shi ne wanda ya jagoranci samar da bankin musulunci wato Ja’ez Bank.