Labarai
Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa
Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu ya rushe majalisarsa bayan kammala wata ganawa da duk masu rike da mukamai a Masarautar.
Babban dan majalisar Sarkin Magajin Garin Karaye Injiniya Shehu Ahmad ne ya sanar da hakan, sai dai ya ce rushewar ba ta shafi wasu Hakimai guda takwas na Masarautar ba.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Karaye Haruna Gunduwawa ya fitar a yau.
An dakatar da hawan Sarki Majalisar masarautar Kano
An yi zangazangar kin amincewa da kara masarautu a Kano
Gwmantin Kano ta musanta yunkurin sauya wa sarkin Kano Masarauta
Sarkin Rano ya dakatar da wasu Hakimai
Sanarwar ta kara da cewa Sarkin ya jaddada aniyarsa ta fadada mukaman a cikin kananan hukumomi 8 na Masarautar, tare da alkawarta cewa wasu daga masu rike da mukaman za su dawo yayin da wasu kuma za a daga likkafarsu.
Ya kuma jinjinawa ‘yan majalisar ta sa bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ciyar da Masarautar ta Karaye gaba.