Kaduna
Sarkin Leren jihar Kaduna Alhaji Abubakar Garba Mohammed ya rasu.
Sarkin Lere a jihar Kaduna, Abubakar Garba Mohammed ya rasu.
Marigayi sarkin ya rasu ne a safiyar Asabar, a Kaduna bayan gajeriyar rashin lafiya, yana da shekara 77.
Rahotanni sun bayyana cewa za a yi jana’zar Abubakar Garba Mohammed a garin Lere da yammacin Asabar din nan da karfe 5 na yamma.
Sarki Abubakar Garba Muhammad wanda ya hau gadon sarauta bayan rasuwar Umaru Sani a shekarar 2011, ya bar ’ya’ya hudu da jikoki da dama.
An haife shi ne a ranar 15 ga Afrilu, 1944, kuma ya halarci makarantar firamare ta Lere da Soba tsakanin 1951 da 1958 kafin ya wuce Kwalejin Barewa fa ke Zariya daga 1959 zuwa 1963.
Marigayi Abubakar Garba Mohammed ya kasance a Jami’ar Ahmadu Bello tsakanin 1965 da 1966 kafin ya ci gaba zuwa Kwalejin Kwalejin Fasaha ta California da ke Amurka bayan haka ya shiga aikin soja a Najeriya.
Kafin rasuwar sa ya rike mukamai har zuwa mukamin birgediya janar kuma ya kasance mai kula da harkokin soja a jihar Sakkwato daga watan Agusta 1985 zuwa Satumba 1986.
You must be logged in to post a comment Login