Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Sarkin Muslim ya bukaci gwamnatin tarayya samar da hanyoyin dakili matsalolin siyasa da addinai

Published

on

Mai alfarma sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya bukaci gwamnatin tarayya da ta fito da wasu dabaru na zamani wajen magance matsalolin da ke kunno kai tsakanin bangaren siyasa da kuma na addinai.

 

Sarkin Musulmin ya yi wannan kiran ne a jiya yayin kaddamar da wani littafi mai sahfi 240 da kungiyar da ke rajin ci gaban addinin musulunci ta MURIC ta gabatar jiya a birnin tarayya Abuja.

 

Sarkin musulmin da ya samu wakilicin sarkin Keffi Dr Shehu Chido Yamusa na III ya nuna matukar damuwa kan yadda ake yin amfani da addini wajen al’amuran siyasa, a maimakon yin amfani da shi a matsayin wanzar da zaman lafiya.

 

Sarkin ya kuma bukaci kungiyar ta MURIC da ta ci gaba da yada da’awa a akan addinin musulunci musamman kira kan zaman lafiya da sauran al’amura.

 

A cewar sa nuna banbaci a tsakanin mabiya addinin islama da rashin kwantar da hankalin jama’a a matsayin abin da ke kawo cikas wajen hadin kan yan uwa musulmi

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!