Addini
Sarkin Musulmi ga Buhari da gwamnoni: Ku gaggauta kawo ƙarshen zubar da jinin jama’a
Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya buƙaci shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da gwamnonin ƙasar nan da su yi duk me yiwuwa don kawo ƙarshen zubar da jinin jama’a babu gaira babu dalili da ke faruwa a sassa daban-daban na Najeriya.
Sarkin na musulmi yayi wannan kiran ne jim kadan bayan kammala sallar idi jiya a Sokoto.
Ya ce: “Muna kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da kafatanin gwamnonin ƙasar nan da su yi duk me yiwuwa wajen ganin sun magance matsalar rashin tsaro da ke addabar ƙasar nan’’
‘‘A matsayin ku na shugabannin mu wajibi ne ku zage dantse ku jajirce don ganin wannan matsala ta zo ƙarshe’’ acewar sarkin musulmin.
Sarkin na musulmi ya kuma buƙaci al’ummar musulmi da su yi addu’oi ga shugabannin su wanda hakan zai taimaka musu wajen daƙile matsalolin da ke damun ƙasar nan a wannan lokaci.
You must be logged in to post a comment Login