Addini
Sarkin Musulmi ya ayyana Laraba a matsayin daya ga Zul-hijja

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana yau Laraba, 28 ga watan Mayu da muke ciki a matsayin ranar daya ga watan Zul-hijja na shekarar 1446 bayan Hijira.
Sarkin Musulmin, wanda shi ne shugaban Majalisar kolin addinin Musulunci, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta babban mashawarcinsa na musamman kan harkokin addini Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanya wa hannu.
Wannan sanarwa dai na nufin za a yi idin babbar Sallah a Najeriya a ranar Juma’a 10 ga watan na Zul-hijja, wadda ta yi dai-dai da 6 ga watan Yunin bana.
Wannan dai na zuwa ne dai-dai da ganin watan a kasar Saudiyya, wadda tun farko ta ayyana Laraba a matsayin ranar daya ga watan na Zul-hijja, tare da cewa za a hau Arfa a ranar Alhamis, 5 ga watan Yuni.
You must be logged in to post a comment Login