Labarai
Sarkin Musulmi ya kalubalanci jami’an tsaro wajen gaza kan kawo karshen kashe-kashen tsakanin makiyaya da manoma
Mai alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’adu Abubakar III ya kalubalanci nagartar da jami’an tsaron Najeriya ke da ita, da kuma gaza kawo karshen kashe-kashen dake faruwa tsakanin Fulani makiyaya da manoma a jihar Benue.
Sarkin Musulmin ya ce ya kamata jami’an tsaro su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen wannan matsala, inda ya gargadi malaman addinai da yan siyasa, da su guji furta kalaman da ka iya tunzura mutane domin gudun kazantar al’amarin.
Muhammad Sa’ad Abubakar wanda shi ne shugaban majalisar koli kan addinin Musulunci ya furta hakan ne a jiya Alhamis a birinin tarayya Abuja yayin taron zauran tattaunawa tsakanin addinai mai taken zama tare cin nasara tare.
Ya kuma ce ya kamata a ce al’ummar kasar nan suyi la’akari da rayukun da ke salwanta a kowace rana mai makon rikicin addinai da na kabilanci inda ya ce All.. na fushi ga duk wanda ya kashe wani ba da hakki ba.
Ko da ya ke Sarkin Musulmin ya amici da cewar shi ne babban uban kungiyar Fulani makiyaya ta Miyatti Allah, amma ya ce ba duka Fulani kungiyar ke da iko da su ba duba a cewar mafiya yawan masu laifin a daji ke rayuwa.
Sarkin Musulmi wanda ya ce ko kadan baya nadamar Kasancewar sa Fulani ya alakanta kalaman da babban Sakataren kungiyar mabiya addinin kirastanci, yayi na cewar a rushe kungiyar ta Myatti All.. a kuma ayyanata a matsayin kungiyar yan ta’adda da cewar kalaman muna kiyayya ne ga wani jinsi.