Labarai
Sarkin Zazzau ya umarci Mata masu juna biyu su rika zuwa ganin likita

Mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya bukaci Mata masu juna biyu a fadin jihar Kaduna da su rika zuwa ganin likita don samun ilimin yadda za su haihu cikin koshin lafiya.
Sarkin ya yi wannan kira ne a taron tattaunawa kan harkokin kiwon lafiya a jihar Kaduna.
Haka kuma Sarki Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya jaddada muhimmancin rawar da masarautu ke taka wa wajen karfafa wa al’umma gwiwa a fannin neman ingantacciyar lafiya musamman wajen rage yawan mutuwar mata masu juna biyu da kuma kananan yara.
You must be logged in to post a comment Login